Jan 22, 2019 12:56 UTC
  • An Hallaka 'Yan Ta'adda Biyu A Libiya

Dakarun tsaron Libiya sun sanar da hallaka 'yan ta'adda biyu a gabashin kasar

Kafar watsa labaran Rusiya Al-yaum ta nakalto majiyar tsaron Libiya na cewa dakarun tsaron kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda biyu da suka hada da Umar Juma'ah Asha-alany da Muhamad Attashany a garin Dernah na gabashin kasar.

Rahoton ya tabbatar da cewa Sha'alani da Attashany jigo ne a wasu kungiyoyin 'yan ta'adda ne, to saidai dakarun na Libiya ba su bayyana ce 'yan ta'addar da aka hallaka ko na wata kungiyar 'yan ta'adda ce ba.

Kasar Libiya dai ta fada cikin rikici yaki tun bayan borin da matasan kasar suka yi a shekarar 2011, inda kasar Amurka da Dakarun tsaron Nato suka shiga kasar suka kuma kashe marigayyi kanal Mu'amar Kaddafi.

Tags

Ra'ayi