Feb 04, 2019 19:20 UTC
  • Tashin Bam Ya Ci Rayukan Mutum 11 A Somaliya

'Yan sandar kasar Somaliya sun sanar da mutuwar mutum 11 sanadiyar tashin Bam a Magadushu babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto hukumar 'yan sandar kasar Somaliya na cewa a wannan  Litinin wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a wata cibiyar kasuwanci dake birnin Magadushu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutune 11.

Har ila yau rahoton ya ce ko baya ga mutanan da suka hallaka a harin na yau litinin, akwai wasu 9 na daban da suka jikkata.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, to saidai so dama kungiyar ta'addancin nan ta Ash-shabab mai alaka kut da kut da kungiyar AlQa'ida na daukan alhakin kai irin wadannan hare-hare na ta'addanci a kasar.

Tun a shekarar 2007, kungiyar Ash-shabab ke kokarin wargaza gwamnatin Somaliya da kuma kafa daularta a kasar, to saidai a shekarar 2011, dakarun tsaron kasar Somaliyan da dakarun sulhu na kungiyar tarayyar Afirka sun samu nasarar fatattar mayakan Ash-shabab din daga birnin Magadushu da kuma wasu manyan buranan kasar.

A halin da ake ciki dai, har yanzu kungiyar Ash-shaban din na rike da wasu kauyuka na kudancin kasar.

Tags

Ra'ayi