Feb 15, 2019 19:09 UTC
  • Masu Sanya Ido A Zaben Shugaban Kasa A Najeriya Sun Yabawa Hukumar Zabe

Masu sanya ido daga kasashen waje a zaben shugaban kasa wanda za'a gudanar Gobe Asabar a tarayyar Najeriya sun yada da shirin da hukumar zabe kasar ta yi na gudanar da zabe mai inganci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Nan na Najeriya ya bayyana cew masu sanya ido a zaben na gobe wadanda suka hada da kasar Afrika ta Kudu da kuma na kungiyar Pan Womens Project sun isa birnin Kano a yau Jumma'a , kuma sun ganewa idanunsu wasu shirye-shiryen da hukumar zaben ta tanadar don zaben na gobe. 

Shugaban tawagar masu sanya idan Belinda Madona ta bayyanawa yan jarudu a kano kan cewa kungiyarta ta saba sanya ado a zabubbuka a tarayyar Najeriya kuma tana nan a lokacinda aka gudanar da zaben na shekara ta 2015 sannan a baya-bayan nan ta ga yadda aka yi zabe a jihar Osun da kuma na jihar Iiti. 

Madona ta kara da cewa hukumar zabe ta yi kokari sosai don ganin zaben na bana ya sami nasara, sannan ta yi kira ga yan Najeriya su nuna dattaku a lokacin zabe don ganin zaben ya wuce ba tare da samun wata matsala ba. 

Banda haka ta kira jami'an tsaro da su gudanarv da ayyukansukamar yadda ya dace. 

 

Tags

Ra'ayi