Feb 16, 2019 11:19 UTC
  • Zimbabwe: Masu Hakar Ma'adanai Kimanin 60 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun ce akalla mutane 60 sun rasa rayukansu a daren jiya Juma'a, sakamakon ballewar wata babbar madatsar ruwa a yankin Kadoma.

Majiyoyin gwamnatin kasar ta Zimbabwe sun sanar da cewa, babbar madatsar ruwa ta Kadoma da ke tazarar kilo mita 140 a kudancin birnin Harare wanda haka ya jaza ambaliyar ruwa a yankin, inda aka tabbatar da mutuwar mutane akalla 60 da suke gudanar da aikin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a kusa da madatsar ruwan.

Dubban mutanen dai a kowane suke gudanar da ayyukan hakar ma'adanai da suka hada da zinariya da kuma lu'u-lu'u a kusa da wannan madatsar ruwa, wadanda kuma su ne ambaliyar ruwan tafi shafa.

Gwamnatin Zimbabwe ta ce a cikin shekara ta 2018 da ta gabata, masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a kasar, sun hako zinariya da ta kai tan 20, wanda ya kai kusan kashi na yawan zinariyar da gwamnati ta hako a cikin shekarar ta 2018, wanda ya kai tan 33.

 

Ra'ayi