Feb 16, 2019 16:26 UTC
  • Harin Boko Haram Ya Yi Ajalin Sojojin Nijar 7

Jami'an tsaron Nijar 7 suka rasa rayukkansu a harin da mayakan Boko haram suka kai da yammacin jiya Juma'a a garin Shetima Wangu dake jihar Diffa.

Sanarwar da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar, ta kuma ce akwai wasu jami'an tsaro shida da suka samu raunuka na harsashin bindiga.

A bangaren maharan an hallaka da dama daga cikinsu, an kuma kamo guda 8 daga cikinsu, da motoci uku masu dauke da manyan bindigogi, kirar 12/7/M/M da kuma bindigogi AK47 guda uku, da dumbin harsashai iri daban daban.

Tuni aka shiga biyar sahun maharn inji sanarwar, wacce kuma ta mika ta'aziyarta ga iyallen wadanda suka rasu da kuma fatan sauki cikin sauri ga wadanda lamarin ya rusa dasu da sunan shugaban kasar.

Jihar Diffa mai makobtaka da tarayya Najeriya ta jima tana fuskantar hare haren mayakan kungiyar Boka haram.

Ra'ayi