Feb 19, 2019 16:13 UTC
  • Uganda : Shugaba Museveni Ya Baiwa Dansa Babban Mukamin Soji

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda, ya yi wa dansa karin matsayin soji zuwa mukamin laftana janar, mukami na biyu mafi girma na aikin soji a kasar.

Dama dai kafin hakan ana ganin Laftana janar, Kainerugaba Muhoozi, a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa shugaba Musevenin, duk da cewa shugaban mai shekaru 74 na ci gaba da musanta sanya dan nasa a cikin harkokin siyasa ko kuma ya zama magajinsa.

Bayanai sun nuna cewa a cikin shekaru shida da suka gabata, an yi wa dan shugaban karin matsayi har sau uku a cikin aikin soji. 

Wannan karin matsayin ya sanya Muhoozi, na daf da matsayin mahaifinsa wanda shi janar ne.

Ana dai ci gaba da aza ayar tambaya akan ko dan shugaban, ya cencenci wannan matsayin, duk da cewa ya yi zama kwamandan rundinar musamman ta kasar Uganda.

Ko baya ga dan shugaban an yi wa wasu sojojin kasar 2,000 karin matsayi na gaba.

Shugaba Museveni, wanda aka sake zaba a watan Fabrairu na 2016 a wani wa'adin mulki na biyar, ya shafe shekaru 33 yana shugabancin wannan kasar ta Uganda. 

Tags

Ra'ayi