Feb 19, 2019 16:28 UTC
  • AU Ta Bukaci A Jinkirta Janye Dakarun (AMISOM) A Somalia

Kungiyar tarayyar (AU) ta yi kira da a bi sannu a hankali game da shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiya na AU dake aiki a Somaliya cewa da (AMISOM).

Jami'in kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU shi ne yayi wannan kiran a lokacin taro neman amincewa da yarjejeniyar ayyukan zaman lafiya ta (CONOPS) na ayyukan dakarun AMISOM na shekarar 2018 zuwa 2021.

A kudirin dokar kwamitin sulhun MDD mai lamba 2431 wanda aka amince da shi a shekarar 2018, ta bukaci a rage adadin dakarun tsaron, bayan rage adadin dakarun na farko da aka gudanar a watan Disambar 2017. 

Sabuwar yarjejeniyar, wadda ke tafiyar da ayyukan AMISOM a tsawon wa'adin aikinta tsakanin 2018-2021, zai kawo karshen wa'adin aikin tawagar tsaron ta AU, inda za ta fice baki daya daga kasar ta Somalia.

 

Ra'ayi