Feb 23, 2019 06:59 UTC
  • Sudan: Albashir Ya Rusa Gwamnati Tare Da Kafa Dokar Ta Baci

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya rusa gwamnatin kasar, tare da kafa dokar ta baci a dukkanin fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya gabatar da wani jawabi a jiya wanda aka watsa kai tsaye a dukkanin gidajen radio da talabijin na kasar Sudan, inda ya sanar da rusa majalisar ministoci da kuma gwamnatocin jahohin kasar, tare da kafa dokar ta baci har tsawon shekara guda a dukkanin fadin kasar.

Albashir ya bayyana cewa ministocin harkokin waje, da na tsaro gami da na shari'a za su ci gaba da kasancewa  akan mukamansu, yayin da kuma ya nada wasu manyan jami'an soji 16 da kuma wasu manyan jami'an 'yan sanda 2 a matsayin kantomomi a dukkanin jahohin kasar 18.

A nasu bangaren 'yan adawa sun ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin neman Albashir ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar, wadda ya kwashe shekaru 30 a kanta.

Rahotanni sun ce jami'an 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga-zanga a yankin Ummu Durman.

 

Ra'ayi