Mar 19, 2019 06:19 UTC
  • Mutanen Da Suka Mutu Mozambique Da Zimbabwe Ya Haura 1000

Adadin wadanda suka rasu sanadiyyar guguwar kasashen Mozambique da Zimbabwe sun haura 1000.

Guguwar da aka bai wa sunan Idai ta kada a kasar Mozambique tare da haddasa razana da tsoro, a tsakiyar kasar. Mahukuntan kasar sun ce adadin mutanen da su ka kwanta dama sun haura 1000.

A can kasar Zimbabwe mai makwabtaka da Mozambique kuwa, mahukunta sun ce adadin mutanen da su ka kwanta dama sun kai 89, yayin da wasu 150 su ka bace.

Birnin Beira na kasar Mozambique ya fuskanci barna mafi girma, kamar yadda hukumar agaji ta “Red Cross’ ta ce; kaso 90% na birnin ya rushe.

Shugaban kasar Mozambique Felipe Nyusi ya ce; Da fari sun tattara bayanai na mutuwar mutane 84, amma daga baya da mu ka yi amfani da jiragen sama domin ganin barnar da ta faru, dalilai sun tabbatar da cewa fiye da mutane 1000 ne su ka kwanta dama.

 

 

 

Ra'ayi