• Muhammad Jawad Zarif A Guinea Conakry
    Muhammad Jawad Zarif A Guinea Conakry

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya kammala ziyarar aiki da ya gudanar a yammacin nahiyar Afirka, wadda ya fara tun daga daren Lahadin da ta gabata, inda ya fara isa birnin Abuja na tarayyar Najeriya a matsayin zangon farko na ziyarar tasa.

A yayin ziyarar tasa a Abuja, Zarif ya gana da manyan jami'an Najeriya, da suka hada da shugaban kasar Muhammad Buhari, gami da ministan harkokin waje da kuma shugaban majalisar dattijai, kamar yadda ya gana da manyan jami'ai a bngaren harkokin tattalin arziki da cinikayya na Najeriya.

Kamar yadda kuma bayan kammala ziyarar tasa daga tarayyar Najeriya ya isa birnin Akra na kasar Ghana, inda a can ma ya gana da manyan jami'an gwamnatin kasar, da suka hada da shugaba Drmani Mahama, gami da sauran jami'ai da suka hada da ministar harkokin wajen kasar Hanna Tetteh da kuma shugaban majalisar dokokin Edwad Adajahu, kamar yadda kuma Zarif ya jagoranci wani shiri na dashen itace a kasar ta Ghana.

Bayan kammala ziyarar tasa a Ghana a ranar Laraba, Zarif ya isa birnin Conakry fadar mulkin kasar Guinea Conakry, inda a can ma ya gudanar da tattaunawa tare da manyan jami'an kasar da suka hada da shugaban kasar Alfa Conde, da kuma firayi ministan kasar Mamadi Yula, da kuma shugaban majalisa da kuma ministocin harkokin waje da na tattalin arzikin kasar.

A jiya Alhamis Zarif ya isa birnin Bamaku na kasar Mali, a matsayin zangon karshe na ziyararsa, inda a ya gana da manyan jami'an gwamnatin kasar, da suka hada da firayi minister Modibo Keita, da minitan harkokin waje da kuma shugaban majalisa.

Babban abin da ziyarar ta Zarif ya mayar da hankali a kansa dai shi ne batun kara bunkasa alaka ta diplomasiyya da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Iran da kasashen yammacin nahiyar Afirka, sai kuma batun noma da hanyoyin yaki da ayyukan ta'addanci musamamn a kasashen Najeriya da kuma Mali, wadanda suke fuskantar barazanar 'yan ta'adda na Boko Haram da kuma Alka'ida, da kuma yadda dukkanin bangarorin za su iya yin aiki tare domin fuskantar wannan hadari, kamar yadda kuma a tarayyar Najeriya daga cikin abubuwan da ya tattauna da jami'an kasar har da batun halin da Sheikh Ibrahim Zakzaky yake ciki, musamman ma bayan samun rahotonni kan matsalolin da yake fama da su, na ido da kuma wani bangaren hannunsa, inda Zarif ya bukaci da a sake shi domin samun damar yi masa magani.

Zarif wanda a yau ne zai iso birnin Tehran bayan kammala wannan ziyara, ya fadi a daren jiya a birnin Bamako cewa, ziyarr tasa ta yi nasara matuka, kuma hakan ya bayar da damar bude wasu shafuka na kara fadada alaka tsakanin Iran da wadannan kasashe masu matukar muhimmanci a nahiyar Afirka.  

 

Jul 30, 2016 04:51 UTC
Ra'ayi