• Jagora:Babu Wani Mai Hankali Da Zai Yi Watsi Da Harkokin Tsaron Kasarsa

Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Ali Khaminaee ya jaddada bukatar kare kasar Iran daga duk wata barazana daga makiya.

Jagoran ya bayyana haka ne a yau Lahadi a lokacinda yake ganawa da manya manyan komandojin dakarun kare juyin juya halain musulunci a kasar, da kuma wasu manya manyan jami'an tsaron kasar. 

Jagoran ya kara da cewa a dai dai lokacinda makiya musamman kasar Amurka suke kara bayyana mummunar halayensu ga kasar bai kamata dakarun juyin juya halin kasar su takaita a kan abinda suke ciki a halin yanzu ba, dole ne su ci gaba da neman sabbin hanyoyin  samarda kariya ga kasar Iran.

Jagoran ya kara da cewa ayyukan dakarun juyin juya halin musulunci sun hada da tallafawa mabukata da kuma ayyukan jinkai, amma duk wadan nan ayyuka yakamat su ci gaba sannan a bayyanawa mutane su.

Ranar 31 ga watan sheharivar na ko wace shekara a kalandar iraniyawa ita ce ranar farko na makon kare kasa, wanda ya zo dai da ranar da tsohuwar gwamnatin kasar Iraqi ta fara farwa kasar Iran da yaki wanda ya kai tsawon shekaru 8 suna fafatawa.

 

Sep 18, 2016 18:19 UTC
Ra'ayi