Nov 01, 2016 05:00 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Nijar Ya Ziyarci Iran

A jiya Litinin ce ministan harkokin wajen jamhuriya Nijar Ibrahim Yakuba ya gana da takwaransa na Iran, Muhammad Javad Zarif a birnin Tehran.

Ministan harkokin wajen Nijar din ya kawo ziyara ne tare da rakiyyar wata babbar tawaga data kunshi 'yan siyasa.

A yayin ziyara bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi huldar a tsakaninsu.

Ibarhim Yakuba ya fadawa takwaransa cewa kasarsa a shirye take domin bude offishin jakadanci a birnin Tehran.

Shi kuwa a nasa bangare Muhammad Zarif ya yi fatan hadin gwiwa kasashen biyu wajen inganta harkokin noma, gine-gine, ma'adinai, makamashi da dai sauransu.

Tags

Ra'ayi