Feb 27, 2016 14:33 UTC
  • Ministan Cikin Gidan Iran: Sama Da Kashi 60% Na Iraniyawa Sun Fito Yayin Zabe

Ministan cikin gidan Iran Abdul Ridha Rahmani Fadhli ya yaba da irin fitowar da al'ummar Iran suka yi yayin zabubbukan 'yan majalisar shawarar Musulunci da ta kwararrun na kasar ta Iran da aka gudanar a jiya Juma'a, a daidai lokacin da ake ci gaba da fitar da sakamakon zaben.

Ministan cikin gidan na Iran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai da yayi a yau din nan Asabar inda ya ce bisa la'akari da kirga kimanin kuri'u miliyan 33, hakan yana nuni da cewa sama da kashi 60% na mutanen da suka cancanci kada kuri'a ne suka fito yayin wannan zaben, yana mai cewa a nan gaba bayan gama kidayen dukkanin kuri'un da aka kada ne za a iya fadin hakikanin kashi nawa ne cikin dari suka fito zaben.

Hukumar zaben ta Iran dai tana ci gaba da fitar da sakamakon zaben da aka gudanar na larduna daban-daban inda wasu rahotannin suke nuni da cewa a wajaje da dama masu ra'ayin 'yan mazan jiya su ne a kan gaba, duk da cewa dai ana ci gaba da fitar da sakamakon zaben.

A jiya ne dai aka gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin da kuma ta 'yan majalisar kwararru ta jagoranci inda ake sa ran za a zabi 'yan majalisar dokokin 290 da kuma na kwararrun su 88.

Tags

Ra'ayi