Dec 08, 2016 12:18 UTC
  • Sakon Jagoran Musulunci Na Iran, Zuwa Taron Karawa Juna Sani Na Kasa Akan Salla

Jagoran ya ce; wajibi ne a ci gaba da sanar da al'umma muhimmanci salla da matsayinta.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei, ya ce; Sanar da matsayin salla kamar yadda take, wani nauyi ne da ya zama wajibi a sauke shi.

Jagoran, ya aike da sako ne zuwa wurin taron karawa juna sani karo na 25 na kasa akan tsaida salla da aka bude a nan Tehran.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ci gaba da cewa; Samun nutsuwa ta zuci na daidaikun mutane, da hawa kan mikakken tafarki na shiriya, da kuma kyakkyawar rayuwa, ba za su samu ba sai ta hanyar tsaida salla.

Bugu da kari jagoran ya ce; Dukkanin jami'ai, da malaman addini da masu yin wa'azi da koyarwa, da daidaikun mutane, suna da nauyin da ya rataya a wuyansu na tsaida salla.

 

Tags

Ra'ayi