Dec 28, 2016 11:20 UTC
  • Sojojin Iran Sun Ja Kunnen Jiragen Yakin Amurka Da Suka Kusato Wajen Atisayensu

Kakakin atisayen kare sararin samaniyya da dakarun kasar Iran suke gudanarwa a halin yanzu ya bayyana cewar tsawon kwanaki ukun da suka gabata na atisayen, sau 12 suna jan kunnen jiragen yaki da marasa matuka na Amurka da suke kusatowa wajen da ake gudanar da wannan atisayen.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na Iran ya nakalto Birgediya Abbas Pour, kakakin atisayen da aka ba shi sunan Atisayen "Modafe'in Asemane Velayat 7 (wato Atisayen kare sarararin samaniyar Wilaya na 7)  ya bayyana cewar sojojin Amurkan suna ta kokari ne wajen tattaro bayanai dangane da abubuwan da ke gudana a wajen atisayen.

Birgediya Abbas Pour ya ci gaba da cewa: "tsawon kwanaki ukun da suka gabata, sau 12 ana jan kunne da kuma gargadin jiragen yakin Amurkan da su guji kusatowa kusa da inda ake atisayen", don kuwa ba za su ji ta dadi ba matukar suka shigo cikin sararin samaniyyar inda ake gudanar da atisayen.

A shekaran jiya Litinin ne dai aka kaddamar da wannan atisaye na hadin gwiwa tsakanin sojojin kasa na Iran da bangaren kare sararin samaniyya na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran a kudancin kasar da nufin kare sararin samaniyyar Iran din daga duk wata barazana ta makiya.

 

Tags

Ra'ayi