• Iran : Dubban Al'umma Na Halartar Sallar Jana'izar Ayatollah Rafsanjani

A Jamhuriya musulinci ta Iran, dubban daruruwan al'ummar kasar ne ke tururuwa zuwa babban masallacin Juma'a na kasar dake Tehran babban birnin kasar domin halartar sallar jana'izar Ayatollah Hashimi Rafsanjani wanda Allah yayi wa rasuwa a ranar Lahadi data gabata.

Jagoran juyin juya halin musulinci na kasar ne Ayatollah Sayyid Ali Khamenei zai jagoranci sallar jana'izar mirigayin wace kuma mayan malamai na  kasar da jami'an gwamnati zasu halarta.

Za'a dai bizne Mirigayin a hubbaren Imam Khomaini dake Tehran babban birnin kasar a yau Talata.

kafin hakan dai an shiga zaman makoki na kwanaki uku domin juyayin rasuwar tsohon shugaban kasar wanda shi ne shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin muslunci ta Iran.

Da yammacin Ranar Lahadi ne Allah ya yi wa Ayatollah Rafsanjani rasuwa sakamakon matsalar zuciya.

A rayuwarsa Ayatollah rafsanjani ya rike mukamai da dama daga ciki kuwa har da shugabancin kasar ta Iran daga shekarar 1989 zuwa 1997.

Jan 10, 2017 06:34 UTC
Ra'ayi