Bayan kammala gudanar da sallar mamaci a kan gawar tsohon shugaban kasar Iran Ayatollah Hashimi Rafsanjania dazu a masallacin jami'ar Tehran, ana ci gaba da gudanar da jana'izarsa zuwa hubbaren marigayi Imam Khomenei da ke wajen birnin Tehhran.

Dubban daruruwan jama'a ne da suka hada da manyan jami'an gwamnatin Iran da kuma jami'ai daga kasashen ketare gami da jakadun kasashen waje da ke Iran suke halartar jana'izar tashi a yau.

Ayatollah rafsanjani dai ya kasance daya daga cikin manyan na hannun damar marigayi Imam Khomenei, kuma daya daga cikin wadanda suka taka gagarumar rawa wajen kafa juyin Islama a kasar Iran, kamar yadda kuma ya rike manyan mukamai bayan samun nasarar juyin, da suka hada da shugaban kasa, shugaban majalisar dokoki, da kuma wasu mukamai na daban, ya rasu yana da shekaru kusan 83.

Jan 10, 2017 12:25 UTC
Ra'ayi