• Zaman Ta'aziyyar Ayatollah Rafsanjani Tare Da Halartar Jagora

An fara zaman ta'aziyyar Ayatollah Hashimi Rafsanjani a Husainiyyar Imam Khomeni (RA) tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

A zaman ta'aziyar, dangin marigayin tare da manyan jami'an gwamnatin Iran da suka hada da shugaban kasa da kuma shugaban majalisar dokoki gami da babban alkalin alkalai, gami da sauran dubban mutane daga ko'ina da suke halartar wurin.

A farkon zaman dai an bude wurin da karatun kur'ani mai tsarki, da kuma karato wasu daga cikin bayanai na manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka.

A jiya ne dai aka gudanar da janazar Ayatollah Hashimi rafsanjani, wanda jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranta, an kuma bizne gawar tasa ne a cikin hubbaren marigayi Imam Khomenei (RA) da ke kudancin birnin Tehran

Jan 11, 2017 11:19 UTC
Ra'ayi