Apr 02, 2017 04:54 UTC
  • Larijani: Pentagon Da CIA Su Ne Manyan Masu Daure Wa Ta'addanci Gindi

Shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani yayi kakkausar suka ga tsoma bakin da Amurka take yi cikin lamurran cikin gidan kasashen Gabas ta tsakiya yana mai cewa Amurkan tana da alaka ta kut da kut da dukkanin ta'adda da kuma ta'addancin da ke faruwa a yankin.

Dakta Ali Larijani ya bayyana hakan ne a watani jawabi da yayi a jiya Asabar inda ya ce: Sojojin Amurka, Ma'aikatar tsaron kasar Pentagon da kuma hukumar leken asirin Amurkan, CIA su ne masu daukan nauyin 'yan ta'addan da suke yankin nan  da kuma ci gaba da yin kafar ungulu ga tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankin.

Don haka sai shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran din ya ce 'yan majalisar za su ci gaba da sanya ido kan abin da ke faruwa da kuma daukar matakan da suka dace kan wannan lamarin

Kalaman shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran din sun zo ne a daidai lokacin da wasu 'yan majalisar Amurkan suke kokari wajen kafa wata doka da ta umurci ma'aikatar wajen Amurkan da ta sanya dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) cikin jerin kungiyoyin ta'adanci.

 

Tags

Ra'ayi