Mayu 23, 2017 05:53 UTC
  • Iran Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar  Da Sayar Da Makamai Ga 'Masu Goyon Bayan Ta'addanci

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kirayi Amurka da ta yi watsi da siyasarta ta neman hada fada, tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe, sanya tsoron Iran cikin zukatan kasashe da kuma sayar da makamai masu hatsari da manyan masu goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran Bahram Qassemi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai Saudiyya da kuma yarjejeniyar sayar mata da makamai da biliyoyin daloli da aka cimma yayin ziyarar inda ya ce abin bakin ciki ne yadda Amurka take ci gaba da karfafa kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Gabas ta tsakiya da kuma gwamnatocin kama-karya da suke goyon bayan wadannan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Har ila yau Mr. Qassemi yayi watsi da zargin da Trump din yayi na cewa Iran tana ba da kudade, makamai da kuma horar da kungiyoyin 'yan ta'adda da masu tsaurin ra'ayi don haifar da rashin tsaro a yankin Gabas ta  tsakiyan inda ya ce abin mamaki ne yadda kasar da take goyon yahudawan sahyoniya wajen ci gaba da ayyukan ashsha da zalunci kan al'ummar Palastinawa amma ita ce take zargin Iran da kokarin dagula lamuran yankin Gabas ta tsakiya yana mai ishara da irin goyon bayan da gwamnatin Amurkan take ba wa kasashen da suke ci gaba da zubar da jinin al'ummar Yemen da kuma goyon bayan kungiyoyin ta'addanci irin su ISIS da Al-Nusra Front.

A ranar Asabar din da ta gabata ce dai shugaban Amurkan Donald Trump, yayin ziyarar da ya kai Saudiyya, ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar sayar da makamai wa Saudiyyan da ta kai ta Dala biliyan 110.

 

Tags

Ra'ayi