• Iran : Zarif, Ya Fara Ran Gadi A Arewacin Afrika

Yau Lahadi, ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif, ya fara wani ran gadi a wasu kasashen arewacin Afrika.

Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta farko da Mista Zarif zai kai a arewacin Afrika, inda zai ziyarci kasashen da suka hada da Aljeriya, Mauritaniya da kuma Tunusia. 

Babban jigon wannan ziyara ta kwanaki biyu shi ne tattauna huldar dake tsakanin Iran da wadanan kasashen uku da kuma batutuwan da suka shafi halinda ake ciki a yankin gabas ta tsakiya a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Bahram Qassemi.

Ana sa ran kuma bangarorin zasu tattauna batun kasar Syria da kuma na kasashen yakin tekun Pasha, da nufin samar da hadin kan kasashen musulmi a daidai lokacin da rikicin diflomatsiya ya kunno kai a tsakanin wasu kasashen yankin a cewar Mista Qassemi.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran dai ta bukaci kasashen musulmi dasu hada kai waje daya domin kaucewa duk wani sharri na makiya.

 

Jun 18, 2017 14:02 UTC
Ra'ayi