• Wani Babban Kwamandan ISIS Ya Halaka A Harin Da Iran Ta Kai A Syria

Daya daga cikin manyan kwamnadojin kungiyar 'yan ta'addan takfiriyya ta (Daesh) ISIS ya halaka sakamakon harin da Iran ta kaddamar a jiya a kan sansanonin 'yan ta'adda a Syria.

Kamfanin dillancin labaran IRIB ya bayar da rahoto daga Syria cewa, wasu majiyoyi masu tushe daga fagen daga a kasar Syria sun tabbatar da cewa, Sa'ad Al-husaini dan kasar Saudiyyah, wanda aka fi sani da Abu Sa'ad, daya daga cikin manyan jagororin kungiyar ISIS, yana daga cikin manyan kwamandojin kungiyar 'yan ta'addan na ISIS da suka halaka a daren jiya, bayan saukar makaman ballistic da dakarun IRGC suka harba daga cikin kasar Iran zuwa kan sansaninsu da ke Deir Zur a cikin kasarSyria.

Dakarun na IRGC sun ce wannan somin tabi ne na alwashin da suka sha na mayar da martani da daukar fansa a kan harin da kungiyar ISIS ta kai a Tehran, kuma akwai wasu matakan na gaba da suke tafe a kan kungiyar ta ISIS da masu daukar nauyinsu.

Jun 19, 2017 17:24 UTC
Ra'ayi