• Shugaba Ruhani Ya Mikawa Majalisa Sunayen Wasu Ministocin Da Ya Nada A Sabuwar Gwamnatinsa

Dr Hassan Ruhani, shugaban kasar Iran ya mika wa majalisar dokokin kasar sunayen wasu daga cikin ministocin da ya nada a cikin sabuwar gwamnatinsa a jiya talata.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa a cikin jerin sunayen da shugaban ya gabatarwa majalisar don neman amincewarta a jiya, sun hada da tsoffin fuskoki kamar Mohammad Jawad Zarif a matsayin ministan harkokin waje, Amir Khatami a matsayin ministan tsaro, Bijan Zangane a matsayin ministan man fetur, Abdurrida Rhamani Fadly a matsayin ministan cikin gida da kuma Sayyeed Mahmood Alawi a matsayin ministan yansandan ciki.

Har'ila yau shugaban ya sanya sabbin fuskoki kimani 7 a kujerun ministoci a sabuwar gwamnatin. A halin yanzu dai gwamnatin jumhuriyar musulunci a Iran tana da kujerun ministoci 18. Labarin yana kara da cewa shugaban bai nada ministan ilmi da tarbiyaba sai daga baya. Daga mako mai zuwa ne ake saran majalisar dokoki a nan iran zata fara tantance ministocin da shugaban ya aiko mata.

 

Aug 10, 2017 06:26 UTC
Ra'ayi