Limamin na Tehran da ya ke ishara da muhimmancin ranar tsayuwa a gaban Allah ga dan'adam, ya ce; Daya daga cikin abinda ranar kiyama ta kiyama ta kebanta da shi, shi ne yi wa mutum hisabi.

Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidy Karmani ya ci gaba da cewa; A bisa koyarwar musulunci, ya kamata mutum ya rika yi wa kansa hisabi tun a duniya gabanin ya tsaya domin a yi masa hisabi a lahira.

Limamin juma'ar na Tehran ya kuma ce; A ranar kiyama wasu mutanen za a yi musu hisabi cikin sauki yayin da wasu za su fuskanci hisabi mai tsanani, kowane bisa gwargwadon abinda ya aikata a duniya.

Ayatullah Karmani ya kirayi kanshi da kuma sauran al'ummar musulmi da su ji tsoron Allah da kuma kula da ayyukansu da halayensu a duniya gabanin fuskantar sakamako a lahira.

Aug 11, 2017 11:10 UTC
Ra'ayi