• Ambaliyar Ruwa Ta Lashe Rayukan Mutane Akalla 13 A Kasar Iran

Shugaban hukumar kula da hatsarurruka ta dabi'a a kasar Iran ya sanar da cewa: Ambaliyar ruwan da ta auku a wasu yankunan arewacin kasar ta lashe rayukan mutane akalla 13.

A ganawarsa da manema labarai a yau Asabar; Shugaban hukumar kula da hatsarurruka ta dabi'a a Jamhuriyar Musulunci ta Iran Isma'il Najjar ya fayyace cewa: Ambaliyar ruwan da ta faru a wasu yankunan lardin Ghulistan, Khurasan Ridhawi da Khurasan ta Arewa a jiya Juma'a ta janyo hasarar rayukan mutane akalla 13  tare da bacewar wasu mutane biyu na daban.

Har ila yau ambaliyar ruwan ta janyo lalacewar hanyoyi da gine-gine da hasarar dukiyoyi a yankunan, kuma mutane kimanin 400 ne masifar ambaliyar ta ritsa da su da a halin yanzu haka aka samar musu da matsuguni da kayayyakin jin kai. 

Aug 12, 2017 11:51 UTC
Ra'ayi