• Jagora:  Wajibi Ne A Kare Ruhin Juyi Da Addini A Cikin Ayyukan Diplomasiyya

Ayautullah Sayyid Ali Khamnei ya bayayna haka ne a yayin da ya ke ganawa da shugaban kasa da ministocinsa.

Ayautullah Sayyid Ali Khamnei ya kara da cewa; A cikin aikin diplomasiyya wajibi ne a rika daukar matakai bisa dacewa da abinda yake faruwa, da sauri, kuma bisa aiki da kaifin fahimta.

Har ila yau, jagoran juyin musuluncin na Iran ya kara da cewa; A cikin aikin diplomasiyya a rika dogaro da manufofin juyi da suka hada da yin tsayin daka wajen kalubalantar masu girman kai na duniya, fada da zalunci da jin daukaka.

Jagoran ya kuma fadawa shugaban kasa da 'yan majalisarsa cewa su maida hankali wajen warware matsalar al'umma ta hanyar amfani da ruhin jihadi da kuma rubanya kwazo.

 

Aug 26, 2017 18:53 UTC
Ra'ayi