• Iran Zata Yi Iya Kokarinta Don Ganin An Tsaida Zubar Da Jinin Musulman Myanmar

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin kasar zata bi dukkan hanyoyin da suka kamata don ganin ta kawo karshen zubar da jinin musulman kasar Myanmar.

Bahram Qasimi ya fadawa muryar JMI a wata tattaunawa da shi a yau Talata kan cewa taron shekara-shekara na babban zauren MDD wanda za'a gudanar a karshen wannan watan wata dama ce ta gabatar da batun ga kasashen duniya don magance shi. 

Banda haka Qasimi ya ce tuni ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zareef ta rubutawa babban sakataren MDD wasika kan wannan batun, sannan zai kara tattauna wannan batun da sauran kasashen duniya a taron na shekara-shekara a birnin Newa York.

 Tun shekara 2012 ne sojojin kasar Myanmar da kuma mabiya addinin Buza masu tsatsauran ra'ayin addini suke gallazawa musulman kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu sannan wasu dubban daruruwa suka yo hijira zuwa kasar Bangladesh da kuma wasu kasashen yankin.

 

Sep 12, 2017 18:55 UTC
Ra'ayi