• Jagora: Magance Matsalar Musulmin Kasar Myanmar Nauyi Ne A Kan Kasashen Musulmi

Jagoran juyin juya halin musulionci na kasar Iran ya soki kungiyoyin kasa da kasa da masu da'awar kare hakin bil-adama kan yadda suka yi shuru da kuma rashin daukan mataki game da yadda ake yiwa al'ummar musulmi kisan kiyashi a kasar Myammar.

A jawabin da ya gabatar gabanin fara darasi na fikhu a jiya Talata, jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa ya kamata kasashen musulmi su dauki mataki a kan gwamnatin Myammar, amma ba ma nufin daukan matakin soja da zubar da jini, saidai ya kamata a daukin matakin matsin lamba a bangaren siyasa da tattalin arziki da kuma kasuwanci ga gwamnatin ta Myammar domin ladabtar da ita game da wannan ta'addanci da ta aiwatar a kan al'ummar musulmi.

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kara da cewa taron da kungiyar hadin kan kasashen musulmi suka gudanar a kan matsalar kasar Myammar yayi daidai, kuma Duniyar yau, duniya ce ta zalunci, domin haka abin alfahari ne ga jamhuriyar musulinci ta Iran da take bayyana matsayin ta na yaki da zalunci a ko ina, kama daga irin zaluncin da ake yiwa al'ummar Palastinu, Yemen, Bahrain, da Myammar.

Yayin da yake bayyana yadda ake takaita matsalar kasar myammar kan rikicin addini tsakanin musulmi da mabiya addinin buda, jagora ya bayyana cewa hakan ba gaskiya ba ne, ko da yake akwai yiyuwar kabilancin addini ya nada tasiri a rikcin, to amma wannan matsala ce ta siyasa, domin wacce ke aiwatar da wannan kisa gwamnatin kasar Myammar ce bisa jagorancin Matar da ba ta da imani a zuciyarta kuma wannan mata ita ce ta samu lambar yabo ta zaman lafiya ta nobel, bayan aukuwar wannan lamari, to a hakika kisa ya zamanto lambar yabo ta zaman lafiya a Duniya.

Sep 13, 2017 05:52 UTC
Ra'ayi