• Sharhi: Jagora Yayi Kakkausar Suka Kan Halin Ko In Kula Da Ake Nunawa Musulman Myammar

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi kakkausar suka dangane da shiru da kuma halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa da masu ikirarin kare hakkokin bil'adama suke yi dangane da kisan kiyashin da ake yi wa musulmin kasar Myammar inda ya ce hanyar magance wannan matsalar ita ce kasashen musulmi su dau matakan da suka dace a aikace da kuma yin matsin lamba ta siyasa da tattalin arziki ga gwamnatin kasar Myammar.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a jiya Talata a farkon darasin fikihu (Bahasul Kharij) da yake bayarwa dalibai, inda yayin da yake karin haske dangane da abin da ya ke nufi da shigowar gwamnatocin kasashen musulmi cikin wannan lamarin don magance shi ya ce: Abin nufi da shigowar kasashen musulmi cikin lamarin ba shi ne tura sojoji, face dai wajibi ne su kara matsin lamba na siyasa, tattalin arziki da kasuwanci ga gwamnatin Myammar da kuma nuna rashin amincewarsu da hakan a cibiyoyin kasa da kasa.

Ko shakka babu lamarin Myammar da zaluncin da ake yi wa musulmin Rohingya ci gaba ne na makircin makiya da kuma irin zalunci da kisan kare dangi da ake yi wa musulmi tsawon tarihi; duk kuwa da kokarin da wasu suke yi na ba wa wannan rikicin na Myammar wani bangare na mazhaba da addini.

A saboda haka ne ma yayin da yake bayyana rashin gaskiyar wannan kokari da wasu suke yi na takaita wannan lamari da cewa wani rikici ne na addini tsakanin musulmi da 'yan Budha, Jagoran ya bayyana cewar: Mai yiyuwa ne tsaurin ra'ayi na addini ya zamanto yana da tasiri cikin wannan rikicin, to amma ko shakka babu wannan lamarin wani lamari ne na siyasa. Don kuwa mai gudanar da shi ita ce gwamnatin Myammar, wacce take karkashin ikon wata muguwar mace maras tausayi wacce ta taba cin kyautar zaman lafiya ta Nobel; to amma faruwar wannan lamarin ya kawo karshen wannan kyauta ta zaman lafiya ta Nobel.

Abin bakin cikin shi ne cewa darewa karagar mulkin kasar Myammar din da Aung Sang Suu Kyi ta yi bai sanya rayuwar musulmin Rohingya na kasar ta yi kyau ba, face ma dai ta kara muni ne, hakan kuwa wani lamari ne da dama daga cikin masu sharhi kan lamurran siyasa ko dai suka rufe ido kansa ko kuma suka mance. Abin da a halin yanzu yake faruwa a Myammar ba wai kawai ya takaita da makomar musulman Rohingya miliyan guda da wani abu na kasar ba ne; face dai ci gaba da silsilar makirce-makircen da ake kulla wa Musulunci da musulmi ta hanyoyi da dama da suka hada da kirkiro da ta'addanci da tsaurin ra'ayin addini da sunan Musulunci.

Ko shakka babu cibiyoyin kasa da kasa irin su Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaron majalisar suna da gagarumin nauyi a wuyansu na kawo karshen wannan aika-aika da ake yi wa musulmin Rohingya, duk kuwa da ci gaba da nuna halin ko in kula da suke nuna wa wannan lamarin, hakan ne ma ya sanya Ayatullah Khamenei yayi kakkausar suka ga yadda babban sakataren MDD ya takaita da yin Allah wadai da wannan lamarin inda ya ce: Masu ikirarin kare hakkokin bil'adama, wadanda a wasu lokuta suke kumfan baki saboda an hukunta wani mai laifi a wata kasa, amma sai ga shi sun ki yin komai dangane da kisan kiyashi da tarwatsa dubun dubatan mutanen (musulman) Myammar da ake yi.

Irin wannan halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa suke nunawa ne ya sanya nauyin da ke wuyan gwamnatoci da al'ummar musulmi dangane da musulmin Myammar ya ke kara yawa da kuma girma da wajibi ne su sauke shi.

Sep 13, 2017 06:07 UTC
Ra'ayi