Oct 01, 2017 19:16 UTC
  • Juyayin Ashura Ya Game Dukkan Yankunan Kasar Iran A Yau Lahadi

An gudanar da juyayin ashoora a duk fadin Iran a yau Lahadi wanda yayi dai dai na 10 ga watan Muharram ranar tunawa da shahadar Imam Husain (a) jikan manzon All..(s).

A nan tehran dai an gudanar da wannan juyayin a ko ina, daga cikin har da gidan Jagoran juyin juya halin Musulinci. Mutane masu juyayi sun cika masallatayya da husainiyoyi da kuma wajajen ziyara na iyalan gidan manzon All..(s) a birnin.

A wajen mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) dai ranar Ashoora ranar bakin ciki ne don tunawa da yakin karbala a shekara ta 61 bayan hijira inda sojojin Yazid dan Mu'awiya suka kashe Imam Husain (a) da sahabbansa kimani 72 a kasar Karbala . sannan suka kama sauran zurriyar manzon All..(s) a matsayin fursinonin yaki. Akan karanta yadda yakin ya gudana da kuma yin addu'i'o da ziyarar ashoora da kuma wasannin koikoyo don tunawa da wannan rana.

A duk shekara ana gudanar da wannan juyiyin duk tare da dadewarsa  da faruwarsa, don raya zukata da kuma daukar darasi daga abubuwan da suka farau a lokacin.

Tags

Ra'ayi