• Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Kokarin 'Yan Ta'adda Na Kai Hare-Hare Lokacin Ashura

Ministan tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran Sayyid Mahmoud Alawi ya bayyana cewar jami'an tsaron Ma'aikatar tasa sun sami nasarar dakile wani shiri na kai hare-haren ta'addanci a cikin Iran lokacin Ashura yana mai cewa jami'an tsaron sun kame wani adadi na 'yan ta'addan.

Sayyid Mahmoud Alawi ya bayyana hakan ne a jiya Litinin inda yace jami'an tsaron sun gano da kuma tsare wasu mutane da suke shirin kai hare-haren ta'addanci a yankuna daban-daban na Iran a lokacin da ake gudanar da bukukuwan juyayin Ashura don tunawa da kisan gillan da aka yi wa Imam Husaini (a.s) da sahabbansa a Karbala.

Ministan ya kara da cewa mutanen da aka kama din dai ba 'yan wata takamammiyar kungiya ba ce sai dai kowanensu yana gudanar da aikinsa a matsayin mai cin gashin kansa, yana mai sake jaddada aniyar ma'aikatar tasa ta ci gaba da yin dukkanin abin da za ta iya wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan al'umma.

Tun dai bayan harin ta'addancin da wasu 'yan ta'adda suka kai Hubbaren Marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma majalisar shawarar Musulunci ta Iran din a watan Yunin da ya gabata, jami'an tsaron Iran din suka kara damara a fadar da suke yi da 'yan ta'adda a duk fadin kasar wanda ya zuwa yanzu sun sami nasarar dakile da dama daga cikin shirin da 'yan ta'addan suke da shi na kawo hari.

 

Tags

Oct 10, 2017 05:52 UTC
Ra'ayi