• Shugaban Kasar Faransa Ya Bayyana Shirinsa Na Kai Ziyarar Aiki Zuwa Kasar Iran

Shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa: Ra'ayin kasarsa ya sha bamban da na Amurka kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma zai samu lokaci da ya dace domin gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Iran.

Shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya fayyace cewar shugaban kasar Iran Dr Hasan Ruhani ne ya gabatar masa da gayyatar gudanar da ziyarar aiki zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma zai samu lokacin da ya dace domin amsa goron gayyatar.

A ranar Juma'a da ta gabata ce shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zanta da takwararsa na kasar Iran Dr Hasan Ruhani ta hanyar wayar tarho, inda ya jaddada masa cewa kada a dauki maganganun shugaban kasar Amurka Donald Trump da muhimmanci kan kasar Iran da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma tsakanin manyan kasashen duniya gami da kasar Jamus da Jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda kungiyar tarayyar Turai da Faransa sun dauki alkawarin ci gaba da kare yarjejeniyar tare da ganin an aiwatar da ita. Kamar yadda Macron ya bayyana bukatar Faransa na ganin ta bunkasa alaka da kasar Iran a fuskoki da dama. 

Tags

Oct 16, 2017 08:37 UTC
Ra'ayi