Nov 22, 2017 18:20 UTC
  • Jagora: Iran Ta Kawo Karshen Makircin Kirkiro Kungiyar Daesh Da Amurka Da Sahyoniyawa Suka Yi

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ta samu nasarar ruguza makircin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila da wasu kasashen larabawan yankin Gabas ta tsakiya suka kitsa na kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS).

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a yau din nan da dubun dubatan dakarun sa kai na Iran da ake kira da Basij da kwamandojinsu inda ya ce makiya sun yi kokarin amfani da kungiyar ta'addancin ta Daesh don fada da kungiyoyin gwagwarmaya, to sai dai wadannan matasa masu imani sun shigo fage da ruguza kungiyar.

Jagoran ya bayyana nasarar da aka samu a kan kungiyar Da'esh a Siriya Da Iraki da kuma kawo karshen daular da suka kafa a wadannan kasashe biyu a matsayin wata gagarumar nasara da aka samu albarkacin tsayin dakan dakarun gwagwarmaya.

A shekaran jiya ne dai kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo janar Qasim Sulaimani ya sanar da samun nasara da kawo karshen daular Da'esh din a kasar Siriya cikin wata wasika da ya aike wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei wanda ya dora masa alhakin wannan aikin.

 

Tags

Ra'ayi