• Iran A Shirye Take Ta Yi Fada da Duk Wani Kokari Na Sake Kirkiro Wata Kungiyar Ta'addanci

Babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bayyana jinjinawa nasarar da aka samu a kan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) a kasashen Iraki da Siriya yana mai cewa dakarun kasar Iran a shirye suke su yi fada da duk wani kokari na makiya na kirkiro wata kungiya ta ta'addanci irin Da'esh din.

Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bayyana hakan ne cikin wata wasikar taya murna da ya aike wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei inda ya ce dakarun kasar Iran za su yi dukkanin abin da za su iya wajen ruguza duk wani kokari da makiya za su yi wajen sake kirkiro irin wannan kungiyar ta Daesh a nan gaba.

Janar Baqeri ya kara da cewa duk da cewa ta hanyar nasarar da aka samu a kan kungiyar ta'addancin ta Daesh an kawo karshen wani makirci na Amurka da 'yan amshin shatanta da suke yankin nan, to amma wajibi ne a yi riko da shawara da kuma kiran da Jagoran juyin juya halin yayi na cewa wajibi ne a sanya ido kan makirce-makircen makiya.

Shi ma a nasa bangaren babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran din Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari ya bayyana cewar bai kamata a dauki nasarar da aka samu a kan kungiyar Daesh din a Iraki da Siriya a matsayin karshen kungiyar ba yana mai sake sanar da shirin dakarun kare juyin na fada da duk wani kokari da kungiyar ta'addanci za ta yi na ci gaba da ayyukan ta'addanci.

A kwanakin baya ne dai kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, wanda kuma ya jagoranci fada da Daesh din a Iraki da Siriya, Manjo Janar Qasim Sulaimani, cikin wata wasika da ya aike wa Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya sanar da kawo karshen ikon Daesh a kasar Siriya bayan fatattakarsu da aka yi daga garin Bu Kamal na kasar Siriyan.

 

Tags

Nov 24, 2017 05:16 UTC
Ra'ayi