• Jagora: Makiya Suna Amfani Da Kudi Da Makamai Da 'Yan Korensu Wajen Haifar Da Rikici A Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar makiya al'ummar Iran suna amfani da hanyoyi mabambanta wajen cutar da al'umma da kuma tsarin Musulunci ta kasar.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a ganawar mako-mako da yake yi da iyalan shahidan Iran a yau din nan Talata inda yayin da yake ishara da rikicin baya-bayan nan da ya faru a Iran ya bayyana cewar: Yayin abubuwan da suka faru baya-bayan nan, makiyan al'ummar Iran, ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban da suke da shi ciki kuwa har da kudi da makamai da hanyoyi na leken asiri, sun hada karfinsu waje guda wajen haifar da matsaloli ga tsarin Musulunci na Iran.

To sai dai Jagoran ya bayyana 'ruhin jaruntaka, sadaukarwa da kuma imani' da al'ummar Iran suke da shi a matsayin abubuwan da suka hana makiya din cimma wannan bakar aniya ta su.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar a nan gaba zai yi karin bayani dangane da rikicin baya-bayan nan da ya faru a Iran wadanda makiyan kasar suka haifar da nufin cimma bakar aniyarsu.

Daga karshe jagoran ya jinjinawa sadaukarwar da dakarun Iran suka yi yayin kallafaffen yakin shekaru 8 da tsohuwar gwamnatin Iraki ta kallafa wa Iran yana mai cewa idan da a ce makiya sun sami nasara yayin wannan yakin, to da kuwa yanayin Iran a halin yanzu si ya fi na Libiya da Siriya muni.

 

Tags

Jan 02, 2018 17:10 UTC
Ra'ayi