• An Gudanar Da Jerin Gwano A Garuruwan Iran Don Yin Allah Wadai Da Masu Haifar Da Fitina  A Kasar

An gudanar da zanga-zangogi a garuruwa masu yawa na kasar Iran a yau din nan Talata don yin Allah wadai da tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin cikin gidan kasar da kuma rikice-rikicen da wasu suka haifar a wasu garuruwa na kasar bugu da kari kan nuna goyon bayan ga tsarin Musulunci da ke iko a kasar ta Iran.

Rahotanni sun ce an gudanar da irin wadannan jerin gwano ne na dubun dubatan al'ummar kasar a garuruwan Tehran, Qum, Mashhad, Rasht, Hamedan da dai sauransu inda masu zanga-zangar suke rera taken yin Allah wadai da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma munafukai da suke haifar da fitina a cikin gidan na Iran, kamar yadda kuma masu zanga-zangar wadanda suke dauke da hotunan Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei,  suke rera taken nuna goyon baya a gare shi da kuma tsarin Musulunci da ke iko a kasar.

A bangare guda kuma Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta yi kakkausar suka ga kalaman wasu daga cikin jami'an kasar Amurka musamman shugaban kasar Donald Trump dangane da rikicin baya-bayan da ya faru a kasar tana mai cewa al'ummar Iran ba su ba da wata kima da kuma wani muhimmanci ga kalaman na Trump.

Sanarwar Ma'aikatar harkokin wajen ta Iran ta kara da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya ba da dama ga al'umma da su fito su bayyana ra'ayinsu kan abubuwan da ke gudana ta hanyoyin da doka ta tanada, tana mai cewa jami'an Amurka ba su cancanci su yi magana kan batun kare hakkokin al'ummar Iran ba don kuwa su ne a kan gaba wajen take hakkokin al'ummar na Iran.

 

Tags

Jan 02, 2018 17:12 UTC
Ra'ayi