• Manyan Malamai Sun Yi Kira Kan Fitowar Jama'a A Ranar Tunawa Da Samun Nasarar Juyin Juya Hali A Iran

Manyan malaman addinin Musulunci da al'umma ke komawa gare su a fagen hukunce-hukuncen shari'a sun jaddada yin kira kan fitowar al'ummar Iran a ranar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar.

Ayatullahi Nasir Makarim Shirazi daya daga cikin manyan malamai a Jamhuriyar Musulunci kuma marja'i da ake komawa gare shi a fagen sanin hukunce-hukuncen shari'a a yau Laraba ya jaddada yin kira ga al'ummar Iran kan fitowa domin gudanar da zanga-zangar nuna murnar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran da ake kira da ranar 22 ga watan Bahman.

Ayatullahi Makarim ya bayyana cewa: Juyin juya halin Musulunci a Iran ya sha bamban da sauran juyin juya halin da aka yi a sauran kasashen duniya saboda al'ummar Iran ne zalla suka mike tare da kawo canji a kasarsu ba tare da samun wani tallafi daga manyan kasashen yammacin Turai ba.

Har ila yau Ayatullahi Nuri Hamadani daga cikin manyan malaman a kasar Iran da ake komawa gare shi a fagen sanin hukunce-hukuncen shari'a ya bayyana cewa: Nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran ta sadaukar da tarin abubuwa masu kima; don haka fitowar al'ummar Iran a ranar 22 ga watan Bahman yana fayyace daukaka da karfin kasar Iran ce a idon duniya.

A ranar 11 ga watan Fabrairun shekara ta 1979 ce gwagwarmayar juyin juy halin Musulunci karkashin jagorancin marigayi Imam Ruhullahi Al-Musavi Al-Khomeini ta kai ga samun nasara a kasar Iran.

Feb 07, 2018 18:57 UTC
Ra'ayi