• Babban Kwamandan Rundunar Sojin Iran Ya Ce: Al'ummar Iran Zasu Kunyata Makiyansu

Babban kwamandan rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Al'ummar Iran zasu kunyata makiyansu a ranar bikin tunawa da zagayowar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran.

A jawabin da ya gabatar a cikin daren jiya Alhamis a birnin Qum na kasar Iran: Manjo Janar Sayyid Abdur-Rahim Musawi babban kwamndan rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya fayyace cewa: Al'ummar Iran zasu kunyata makiyansu a ranar bikin tunawa da zagayowar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, kuma a wannan rana shugaban Amurka Donald Trump zai fahimci cewa Iran ita ce tushen juyin juya halin Musulunci.

Manjo Janar Abdur-Rahim Musawi ya kara da cewa: Fitowa zanga-zangar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci da al'ummar Iran zasu yi tana matsayin kunyata makiya Iran ne tare da rusa makirce-makircen da suke kitsawa kan kasar musamman Amurka, masarautar Saudiyya da Haramtacciyar kasar Isra'ila.

A ranar 11 ga watan Fabrairun shekara ta 1979 ne da ta yi daidai da ranar 22 ga watan Bahman shekara ta 1357 hijira shamsiyya al'ummar Iran karkashin jagorancin Imam Khomeini {r.a} suka samu nasarar gudanar da juyin juya hali a kasarsu ta hanyar kawo karshen mulkin kama karya ta gidan sarautar shahin-shahi tare da kakkabe hannun makiya Iran a harkokin gudanar da shugabancin kasar musamman Amurka.

 

Tags

Feb 09, 2018 06:39 UTC
Ra'ayi