Feb 13, 2018 06:33 UTC
  • Shugaba Rauhani: Iran Ba Za Ta Tattauna Da Wata Kasa Kan Makamanta Na Kariya Ba

Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya jaddada matsayin kasar Iran na kin amincewa da duk wani batun gudanar da tattaunawa a kan makanta na kariya.

A wata zantawa da manema labarai a yammacin jiya a birnin Tehran, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, hankoron da Amurka ke yi domin ganin ta sanya batun makaman kariya da Iran take mallaka a cikin batun tattaunawar nukiliya, ba abu ne da Iran za ta amince da shi ba.

Ya ce yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya yarjejeniya ce ta kasa da kasa da kasa, don haka Trump ba shi da hurumin da za iya canja ta.

A cikin lokutan baya-bayan nan dai gwamnatin Amurka ta dagea  kan cewa dole ne a saka batun makaman ballistic na Iran a cikin yarjejeniyar nukiliya, saboda barazanar da wadannan makamai suke yi ga kawayen Amurka na yankin gabas ta tsakiya.

Tags

Ra'ayi