• Zarif: Dole Ne Kasashen Turai Su Matsa Lamba Kan Amurka Domin Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, dole ne kasashen turai su matsa lamba kan Amurka domin ta aiwatar da yarjejeniyar nukiliya da ak cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.

Zarif ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Yves Le Drian a yammacin yau Litinin a birnin Tehran.

Ya ce hakika tun bayan rattaba hannu kan wannan yarjejeniya kasashen turai suna yin aiki da ita, amma kuma Amurka tana wasa da hankulan al'ummomin duniya kan wannan yarjejeniya wadda ita ma ta sanya hannu a kanta, a kan ya ce dole ne kasashen turai su yi amfani da tasirinsu wajen matsa lamba kan Amurka domin ta mutunta wannan yarjejeniya ta duniya.

Zarif ya kara da cewa, Iran za ta ci gaba da yin aiki da wannan yarjejeniya ne kawai, idan dukkanin bangarorin yarjejeniyar sun yi aiki da ita kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.

Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Faransa, ya bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan ci gaba da yin aiki da wanann yarjejeniya, tare da jaddada cewa kasarsa ba ta amince da matsayar Amurka ba a kan wannan batu.

Bayan wannan ganawa, ministan harkokin wajen kasar ta Faransa ya kuma gana da shugaba Hassan Rauhani, inda suka tattauna batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma wasu batutuwan yankin gabas ta tsakiya.

Tags

Mar 05, 2018 17:21 UTC
Ra'ayi