• Bahram Qasemi: Kirkiro Fitintinu Na Siyasa Ba Zai Haifar Da Alhairi Ga Kasashen Musulmi Ba

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi, ya bayyana zarge-zargen da Masar da Saudiyya suka yi wa Iran da cewa hankoron haifar da gaba a tsakanin Kasashen musulmi ba maslaha ce gare su ba.

Bahram Qasemi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai yau, a lokacin da yake tsokaci kan wani bangare na bayanin kammala ziyarar yariman Saudiyya a Masar, inda bangarorin biyu suka zargi Iran da shiga cikin harkokin kasashen larabawa.

Qasemi ya ce wannan zargi ne na siyasa wanda ba shi da wata kima, amma kuma  alokaci guda kokari ne na haifar da gaba da fitina  a tsakanin kasashen musulmi, wanda babu abin da irin wanann siyasa za ta haifar illa ci gaba da kara raunana kasashen musulmi.

Ya kara da cewa hakika wannan babar hidima ce ga manyan kasashe masu kiyayya da musulunci, kuma hakan zai kara baiwa makiyan musulmin damar cin Karensu babu babbaka, domin musulmin sun zubar da kimarsu a gaban su.

Daga karshe ya ce Iran ba ta gaba da wata kasar musulmi, kuma har kullum tana yin kira ne zuwa tattaunawa da fahimtar juna tsakanin musulmi baki daya, tare da samun fahimta da kuma girmama juna, da aikin tare domin ci gaban al'ummar musulmi, maimakon zama 'yan koren kasashe 'yan mulkin mallaka.

 

Tags

Mar 07, 2018 17:15 UTC
Ra'ayi