• Jagora: Siyasar Iran A Yankin Gabas Ta Tsakiya Bata Da Alaka Da Amurka Ko Yammacin Turai

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: A duk inda Amurka ta sanya kafa, to barna da tashe-tashen hankula ne suke kunno kai.

A jawabinsa ga dubban mutanen da suka ziyarce shi domin murnar tunawa da zagayowar ranar haihuwar 'yar fiyayyen halitta Fatimatuz- Zahra {a.s} a yau Alhamis: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i ya maida martani kan maganganun mahukuntan Amurka da na yammacin Turai kan irin gagarumar rawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke takawa a yankin gabas ta tsakiya, yana mai tambayar cewa: Shin Amurka da kawayenta suna da hakkin sai Iran ta nemi izininsu ne kafin ta gabatar da nata gudumawa a yankin?

Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kara da cewa: Duk inda Iran zata sanya kafarta sai ta tattauna da mahukuntan kasar tare da samun izininsu, don haka Iran bata bukatar neman izini ko amincewar Amurka da kawayenta. Wannan jawabi na Jagora yana matsayin martani ne kan zarge-zarge marassa tushe da Amurka da kawayenta na kasashen yammacin Turai suke yi cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana tsoma baki a harkokin kasashen yankin gabas ta tsakiya musamman ganin yadda kungiyoyin gwagwarmaya a yankin suke ci gaba da samun nasara a kan abokan gaba da suke samun goyon baya da tallafi daga Amurka da kawayenta.  

Tags

Mar 08, 2018 19:05 UTC
Ra'ayi