• An Yabi Kasar Iran Kan Taka Gagarumar Rawa A Fagen Hana Yaduwar Ayyukan Ta'addanci

Wani marubuci dan kasar Aljeriya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kungiyoyin gwagwarmya da take goya musu baya sun hada yaduwar ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya.

Montasir O'Barton marubuci kuma shahararren masanin tarihi dan kasar Aljeriya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kungiyoyin gwagwarmaya da suke samun goyon bayan kasar ta Iran sun taka gagarumar rawa a fagen hana yaduwar ayyukan ta'addanci a duniya musamman murkushe kungiyar ta'addanci mafi hatsari a duniya ta Da'ish.

Montasir ya kara da cewa: Yana daga cikin shirin kungiyar ta'addanci ta Da'ish mamaye kasashen Iraki da Siriya da ma Aljeriya amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kungiyoyin gwagwarmayar da take mara musu baya musamman kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon da dakarun sa-kai a kasashen Siriya da Iraki gami da sojojin gwamnatin Siriya suka takawa kungiyar ta Da'ish burki tare da rusa makircin iyayen gijinsu.

Montasir O'Barton ya fayyace cewa: A fili yake cewar kasashen Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila gami da 'yan koransu na kasashen Larabawa suke goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda tare da wadata su da muggan makamai da nufin tarwatsa kasashen da ba su biyayya ga munanan manufofinsu a duniya.

Tags

Mar 12, 2018 19:27 UTC
Ra'ayi