Mar 13, 2018 11:18 UTC
  • An Sake Zaban Ayatullah Jannati A Matsayin Shugaban Majalisar Kwararru Ta Iran

'Yan majalisar kwararru ta kasar Iran wacce take da hakkin zaban Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar da kuma ci gaba da sanya ido kan ayyukansa, sun sake zaban Ayatullah Ahmad Jannati a matsayin shugaban majalisar a karo na biyu.

Yayin da yake sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a yau din nan Talata, daya daga cikin membobin majalisar, Ayatullah Sayyid Ali Asghar Dastghaib ya bayyana cewar an sake zaban Ayatullah Ahmad Jannati a matsayin shugaban majalisar. Har ila yau kuma an zabi Ayatullah Sayyid Mahmud Hashemi Shahroudi a matsayin mataimaki na farko na shugaban majalisar, Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kermani a matsayin mataimakin shugaba na biyu.

Har ila yau kuma an zabi Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami da kuma Ayatullah Abbas Ka'abi a matsayin sakatarorin majalisar.

A safiyar yau ne dai majalisar kwararru ta jagorancin ta Iran ta gudanar da zamanta inda aka gudanar da zaben shugabannin da za su jagoranci majalisar, kamar yadda kuma a yau din babban kwamandan dakaraun kare juyin juya halin Musulunci na kasar ta Iran Manjo Janar Muhammad Ali Jafari ya gabatar da jawabi a wajen taron inda yayi karin haske dangane da yanayin da ake ciki  a yankin Gabas ta tsakiya da kuma irin rawar da Iran take takawa wajen tabbatar da tsaron yankin.

 

Tags

Ra'ayi