Mar 16, 2018 04:41 UTC
  • Jawad Zarif Ya Jaddada Wajabcin Dakatar Da Bude Wuta A Yamen Domin Tallafawa Al'ummar Kasar

Yau tsawon shekaru kimanin uku ke nan da masarautar Saudiyya da rundunar kawancenta na kasashen Larabawa suka kwashe suna kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen lamarin da ya wurga al'ummar kasar cikin mummunan kangin rayuwa.

A cewar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonia Guterres a cikin duk dakikoki 10 yaro guda yana mutuwa a Yamen sakamakon cututtuka da suka ci gaba da yaduwa a kasar da kuma matsalar rashin abinci mai gina jiki saboda killace kasar ta Yamen da wasu gungun kasashen Larabawa karkashin jagorancin masarautar Saudiyya suka yi.

A nashi bangaren shugaban kungiyar bada agajin gaggawa ta duniya ta Red Cross Peter Maurer a lokacin da yake gudanar da ziyarar aiki a Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana tsananin damuwarsa kan irin mummunan halin kunci da al'ummar Yamen suke ciki.

A zantawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Jawad Zarif da shugaban kungiyar bada agajin gaggawa ta duniya ta Red Cross Peter Maurer a birnin Tehran: Muhammad Jawad Zarif ya jaddada cewa: Dole ne a dauki matakin dakatar da bude wuta a kasar Yamen domin samun damar aikewa da kayayyakin jin kai musamman magunguna da kayayyakin abinci ga al'ummar kasar da suke cikin halin kaka-ni ka yi.

Tun a watan Maris na shekara ta 2015 ne masarautar Saudiyya da cikakken goyon bayan kasar Amurka ta fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen tare da killace kasar ta sama da kasa da kuma ruwa domin hana shigar da duk wasu kayayyakin jin kai, kuma babban abin mamaki ganin yadda duniya ta yi shiru babu wani mataki da ta dauka domin kawo karshen wannan bakin zalunci kan jinsin bil-Adama musamman kungiyoyin kasa da kasa.

A filin yake cewa: Yakin wuce gona da iri da aka kaddamar kan kasar Yamen lamarin da ya bude kasuwar sayar da makamai ga kasashen Amurka, Birtaniya da kuma Haramtacciyar kasar Isra'ila. Rahotonni sun tabbatar da cewa: A ziyarar aikin baya-bayan nan da Muhammad bin Salman yarima mai jiran gado na Saudiyya ya kai zuwa kasar Birtaniya; ya kulla yarjejeniyar sayan makamai da mahukuntan kasar na dalar Amurka biliyan 100. Kamar yadda a lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kai ziyarar aiki kasar ta Saudiyya a shekarar da ta gabata aka kulla yarjejeniyar sayarwa Saudiyya da makamai na tsaban kudi dalar Amurka biliyan 110.  

Sakamakon haka matakin da masarautar Saudiyya da kawayenta suka dauka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen tare da killaceta lamari ne da zai kara wurga al'ummar Yamen cikin mummunan kangi musamman ganin yadda matsalar cututtuka da rashin abinci suke kara tsananta a kasar.

Ra'ayi