• Ayatullahi Imami Kashani Ya Ce: Makiya Suna Neman Duk Wata Hanyar Cutar Da Kasar Iran

Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Makiya suna shirya makirce-makirce a bangarori da dama da suka hada da tattalin arziki, siyasa, zamantakewa da al'ada domin ganin sun cutar da tsarin Musulunci da ke jagoranci a kasar Iran.

A hudubar sallarsa ta Juma'a a yau: Ayatullahi Muhammad Imami Kashani ya bayyana cewa: Kunna wutan tarzoma, tashe-tashen hankula, matakin matsin lamba kan harkokin tattalin arziki da na siyasa suna daga cikin makirce-makircen da makiya suke kitsawa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran; yana mai jaddada cewa: Makiya tsarin Musulunci a kasar Iran suna kokarin ganin sun raunana ma'aikatar shari'a, Majalisar Shawarar Musulunci da rundunar tsaron kasar Iran.

Ayatullahi Kashani ya jaddada wajabci hadin kan al'ummar Iran domin kalubalantar duk wani makirce-makircen da ake kitsawa kan kasarsu. Kamar yadda limamin ya jaddada yin kira ga mahukuntan Iran kan karin kokari a fagen warware matsalar tattalin arziki da take ci gaba da addabar kasar.   

Mar 16, 2018 18:48 UTC
Ra'ayi