• Shamkhani: Iran Za Ta Ci Gaba Da Aikinta Na Kera Makaman Kariya Babu Kakkautawa

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani ya gargadi kasshen turai da su yi hattara kada su fada cikin tarkon Amurka da Isra'ila, domin kuwa ba za su iya yin nasara wajen dakatar shirin na kera makamain kariya ba.

Ali Shamkahani ya bayyana hakan ne a yau alokacin da yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Oman Yusuf Bin Alawi da yake gudanar da ziyarar aiki a Tehran, inda ya jaddada cewa babu wata doka ta duniya da ta hana wata kasa ta dauki matakan kare kanta daga duk wata barazana.

Shamkhani ya ce; Amurka tana yin matsin lamba  akan kasashen turai kan su watsi da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimmawa tare da Iran, ta hanyar saka batun makaman kariya na Iran a cikin batun yarjejeniyar, wanda hakan baya daga cikin abin da yarjejeniyar ta kunsa.

Ya ce idan kasashen turai suka fada cikin tarkon Amurka da Isra'ila, to su san cewa Ira ba ta taba amincewa da duk wani batun saka makamanta na kariya a cikin batun yarjejeniyar nukiliya ba.

Mar 17, 2018 19:26 UTC
Ra'ayi