• Jami'an Tsaron Iran Sun Kame Gungun 'Yan Ta'adda A Shiyar Kudu Maso Yammacin Kasar

Rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kame wani gungun 'yan ta'adda a lardin Khuzestan da ke shiyar kudu maso yammacin kasar.

A ci gaba da kokarin da jami'an tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke yi na rusa duk wasu makirce-makirce da kasar Amurka da masarautar Ali- Sa'ud da 'yan koransu ke kitsawa kan Iran musamman kokarin kaddammar da hare-haren ta'addanci a cikin kasar: Jami'an tsaron kasar ta Iran sun yi nasarar kame wani gungun 'yan ta'adda dauke da manyan makamai da kanana ciki har da makamai masu linzami.

Gungun 'yan ta'addan sun tsara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri ne kan wajajen taruwar jama'a musamman a lardin na Khuzestan da nufin kunna wutan rikici a kasar. Jami'an tsaron na Iran sun jinjinawa al'ummar lardin kan irin hadin kan da suke bayarwa domin dakile makircin makiya.

Tags

Mar 18, 2018 06:28 UTC
Ra'ayi