• Shugaba Rauhani Ya Taya Putin Murnar Lashe Zabe

Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran dakta Hasan Rauhani ya tura sakon taya murna zuwa ga takwaransa na Rasha Vladimir Putin game da nasarar da ya samu na zaben shugaban kasar a karo na hudu.

A jiya Lahadi ne  aka gudanar da zaben shugaban kasa a Rasha,bayan kidayar kashi 99, 83 na kuri'un da aka kada Hukumar zaben kasar ta (CEC) ta ce shugaba Vladimir Putin ya sake lashe zaben da kashi 76/6 kuma wannan shi zai bashi damar ci gaba da milkin kasar zuwa shekaru shida masu zuwa.

Cikin wani sako da ya turawa takwaran nasa na kasar Rasha, Shugaba Rauhani ya bayyana fatansa na ci gabata da kyautata alaka tsakanin Tehran da Masco, sannan ya ce Iran a shirye take ta kara karfafa alakarta da kasar Rasha musaman ma a siyasa yankin da  kuma na kasa da kasa.

Shugaba Rauhani ya tabbatar da cewa cikin wannan sabon jagoranci na Shugaba Putin, alakar dake tsakanin kasashen Rasha da Iran za ta bunkasa fiye da shekarun baya.

A karshe Shugaba Rauhani ya bayyana fatansa na nasara da ci gaba ga gwamnati da kuma al'ummar kasar Rasha.

Tags

Mar 19, 2018 18:59 UTC
Ra'ayi