• Ruhani Ya Bayyana Cewa: Hadin Kan Al'ummar Iran Ya Bada Mamaki Ga Makiyar Kasar

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Hadin kan al'ummar Iran a fagen fuskantar makiya ya bada mamaki tare da kara daukaka matsayinsu har a idon makiya.

A jawabinsa ga al'ummar Iran domin taya su murnar shiga sabuwar shekara ta 1397 hijira shamsiyya a yammacin yau Talata: Shugaban kasar Iran Dr Hasan Ruhani ya bayyana cewa: Duk da mummunar fatan makiya kasar Iran amma shekarar da ta gabata ta 1396 hijira shamsiyya ta kasance shekarar da al'ummar Iran suka samu gagarumar nasara a bangarori da dama; Yana mai jaddada cewa; Hadin kan al'ummar Iran ya bada tsananin mamaki ga makiyansu, kuma makiyan sun yi furuci da hakan.

Dr Hasan Ruhani ya jaddada cewa: A kullum burin al'ummar Iran shi ne ganin an samu zaman lafiya da sulhu a duniya. Kamar yadda a shekarar da ta gabata ta 1396 al'ummar suka taka gagarumar rawa ta hanyar sadaukar da rayukansu, zage dantse a fagen diflomasiyya domin kasancewa da al'ummun kasashen Iraki, Siriya da Lebenon da nufin ganin an samu wanzuwar zaman lafiya da sulhu a dukkanin yankin gabs ta tsakiya.

 

Tags

Mar 20, 2018 19:15 UTC
Ra'ayi